Idan har sai na mutu
Translated to Hausa by @HausaTranslatorIdan har sai na mutu,
to ka rayu,
don ka ba da labarina
ka sayar da karikitaina
don ka sayo dan kyalle
da 'yan zarurruka,
(ka yi shi fari mai doguwar jela)
don wani yaro, a wani lungu a Gaza
yayin da yake wa samaniya kallon kurilla
yana jiran babansa wanda ya kufce cikin batoyi-
kuma bai wa kowa bankwana ba
hatta tsokar jikinsa
har ma shi kansa-
zai ga firfilo, firfilona da ka kera, yana tashi sama
ya yi tsammani na dan lokaci cewa mala'ika ne
da zai dawo masa da kauna
Idan har sai na mutu
to hakan ya zama fata
ya zama abin labartawa